Wasu mutane su 15, da suka yi ikirarin cewa su jami’an zabe ne suka afka cibiyar tattara sakamakon zabe ta karamar hukumar Alimosho da ke Legas dauke da makamai, lamarin da ya sa akan dole sojoji suka je cibiyar don korarsu da kuma tabbatar da tsaro.
'Yan dabar sun far wa jami'an zabe da ke aiki a wurin da wukake da sanduna, kamar yadda wani bidiyo da talabijin din Reuters ya nuna.
"Kawai 'yan daba suka fara fitowa da wukake suna dukan duk wani jami'in jam'iyyar Labour," in ji sakataren mazabar Jacob Sulemain bayan da sojoji suka dakile harin.
Ana sa ran sakamakon zaben na shugaban kasa zai kasance mafi kusa da kusa a tarihin Najeriya, inda 'yan takara daga jam'iyyu biyu da suka rike mukamai tun bayan karshen mulkin soja a shekarar 1999 ke fuskantar fafatawar da ba a saba gani ba daga wani dan takara na wata karamar jam'iyya wadda ta fi faran jini a tsakanin matasa masu kada kuri'a.