Da yake tabbatar da batun, jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna, ya ce mutane hudu cikin ‘yan bangan da ake zargi da aikta danyen aikin sun shiga hannu.
“Da misalin karfe hudu na yamma yayin da ake tattara sakamakon kuru’un zabe a ofishin hukumar INEC a karamar hukumar Tudun Wada, labari ya zo cewa wani gungun ‘yan banga masu dimbin yawa sun kai hari a ofishin yakin neman zaben dan takaran NNPP na majalisar tarayya kana suka cinnawa ginin wuta.
“Wasu mutane biyu da ba a gano ko su wanene a cikin wata mota dake tsaye a cikin ginin sun kone kurmus a cikin wutar,” Haruna yana fada a cikin wata sanarwa da aka aikewa ‘yan jarida.
A cewarsa, ‘yan bangan da ake zargin sun kuma tattaru kana suka yi yunkurin tare hanya dake zuwa ofishin INEC, kana ya kara da cewa nan take jami’an tsaro sun gaggauta kai dauki a wurin.
Ya bayyana cewa daya daga cikin ‘yan bangan ya jikata an kuma garzaya da shi asibiti inda ya mutu yayin da yake samun kulawa.
Kakakin na ‘yan sanda ya ce ana nan ana gudanar da bincike a kan batun kana za a gurfanar duk wanda ake zargi a gaban kotu.