Babban Sifeton ‘yan sanda Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ce jami’an tsaro dubu 425, 106 za a tura sassan Najeriya domin samar da tsaro yayin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya.
A ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu za a gudanar da zaben na shugaban kasa a duk fadin kasar.
Sifeton ‘yan sandan na Najeriya ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a hedkwatar hukumar zabe ta INEC da ke Abuja a wani taron manema labarai a ranar Juma’a.
Ya kara da cewa adadin jami’an tsaron bai hada da na dakarun kasar ba.
A cewarsa, jami’an tsaron sun hada da na ‘yan sanda, jami’an Civil Defense, jami’an kiyaye hadurra na FRSC da na hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta NDLEA da jami’an EFCC da sauransu.
Rundunar ‘yan sanda Najeriya ita tafi ba da adadi mafi tsoka inda ta shirya tura jami’ai dubu 310, 973 cikin wannan jimullar.