Jam’yar PNDS Tarayya madugar kawancen jam’iyun hambarariyar gwamnatin Nijar ta musanta zargin hannun tsohon Shugaban kasa Issouhou Mahamadou, a juyin mulkin da soja suka yi wa Mohamed Bazoum a ranar Larabar ta gabata.
NIAMEY, NIGER - A wata sanarwar da ta fitar a ranar Asabar uwar jam’iyar ta ce masu neman maida hannun agogo baya a yunkurin dorewar dimokradiya ne ke wannan ikirari da nufin dakile shirin sake mayar da shugaba Bazoum kan kujerar mulki.
Wannan bayani ne daga sakataren harakokin zaben jam’iyar PNDS Boubacar Sabo a lokacin da yake tanttaunawa da wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma a birnin Yamai.
Ga cikakken rahoto yadda hirar tasu ta kaya:
Your browser doesn’t support HTML5