WASHINGTON, D.C. - Isra'ila ta kai hare-hare ta sama a Gaza da Lebanon da sanyin safiyar Juma'a, a matsayin ramuwar gayya saboda harin rokoki kan Isra'ila da gwamnatin Isra'ila ke dora laifin kan kungiyar Islama ta Hamas.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kuma auna cibiyoyin Hamas da ke kudancin Lebanon a wasu hare-hare da ta kaddamar a ranar Juma'a. Wani gidan talabijin na kasar Lebanon ya ce an samu tashin bom a birnin Tyre da ke kudancin kasar.
Sojojin sun ce suna kara yawan dakaru a kan iyakokin kasar da Lebanon da kuma Gaza "don zama cikin shiri ko ta kwana." A baya-bayan nan dai ana zaman dar-dar a yankin bayan arangamar da aka yi tsakanin 'yan sandan Isra'ila da Falasdinawa a cikin masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus, wuri na uku mafi tsarki na mabiya addinin Islama.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayar a rahoton cewa, an sake arangama a masallacin Al-Aqsa a ranar Juma'a kafin sallar asuba tsakanin 'yan sandan Isra'ila da suka rike da sanduna da kuma Falasdinawa da ke ibada suna rera taken goyon bayan Hamas.
A halin da ake ciki kuma, jami'an Isra'ila sun ce an kashe wasu mata biyu sannan mace guda ta samu munanan rauni sakamakon harin harbi da aka kai kan motarsu ranar Juma'a a yankin yammacin gabar kogin Jordan da ke kusa da unguwar Hamra. 'Yan sanda sun ce suna neman wadanda ake zargi.
A ranar Alhamis, Isra'ila ta ce an kai hare-haren rokoki da dama a Isra'ila daga yankin Lebanon.
Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fada a ranar Juma'a cewa, "martanin da Isra'ila za ta maida, a daren yau da kuma nan gaba zai haifar da babban sakamako."
Amurka, Birtaniyya da kuma Majalisar Dinkin Duniya, yayin da suke amincewa da 'yancin Isra'ila na kare kanta, sun bukaci kada ta wuce gona da iri.