An shirya yarjejeniyar tsagaita wutar za ta fara aiki da misalin karfe 11:30 na dare agogon yankin. Wani jami’in leken asirin Masar ya shedawa kamfanin dillanci labarai na Associated Press cewa bangarorin biyun sun amince da tsagaita wuta. Ya yi magana ne bisa sharadin sakaya sunansa saboda yadda tattaunawar bude tsagaita wutar ta kasance mai sarkakiya.
Tsagaita bude wutar za ta kawo karshen fada mafi muni a Gaza tun bayan yakin kwanaki 11 tsakanin Isra’ila da Hamas a bara, a cewar rahotanni.
Ma’aikatar Lafiya a Gaza ta ce akalla mutane 31 ne suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama, ciki har da yara shida, yayin da Isra’ila ta ce ba ita ce ke da alhakin akalla tara daga cikin wadanda suka mutu.
Rikicin na yanzu ya fara ne lokacin da Isra’ila ta kama wani babban jami’in Isalmic Jihad a makon da ya gabata da kuma kashe wani Bafalasdine mai shekaru 17. Kungiyar Islamic Jihad da ke Gaza ta yi barazanar daukar fansa.
A ranar Jumma’a da ta gabata ne Isra’ila ta kaddamar da wani hari ta sama a zirin Gaza, inda ta kashe kwamandan kungiyar Islamic Jihad.
Tun daga wannan lokacin, kungiyar Islamic Jihad ta harba makamai masu linzami kusan 600 kan Isra’ila, wanda yawanci na’urar harbo makamai masu linzamin Isra’ila ta Iron Dome ta harbor su kasa.
‘Yan Isra’ila da ke zaune kusa da zirin Gaza sun shafe kusan kwanaki ukun da suka gabata suna ruwan bama bomai a matsugunan.