Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Kaddamar Da Sabbin Hare-hare a Zirin Gaza


Adadin mutanen da aka kashe a yankin Zirin Gaza da birnin Kudus ya karu, fada da ake yi tsakanin mayakan kungiyar Hamas da dakarun tsaron Isra’ila da ya ta’azzara a yau Laraba.

Isra’ila ta kaddamar da wani sabon zagayen kai hare-hare ta sama a Gaza da sanyin safiyar Laraba, inda take auna ‘yan sanda da wuraren tsaro.

Harin ya shafi wani ginin mai tsawo da ke da ofisoshi masu yawan gaske. Babu kowa a cikin ginin a lokacin da aka kai harin.

Harin da aka kai a ranar Talata ya shafe wani gini mai hawa da yawa, wanda shi ma ya kunshi ofisoshin kungiyar ta Hamas da dama.

An gargadi mazauna cikin ginin da ke kewaye da su fice tun kafin a ruguza ginin.

Rahotanni sun ce Falasadina sama da 40 aka kashe cikin da kananan yara da mata.

Fiye da wasu 200 sun jikkata a hare-haren.

Dakarun sojojin Isra’ila sun ce wuraren da suka auna, ofisoshin leken asiri da gidajen shugabannin Hamasne.

A daya bangaren kuma an kashe Yahudawa shida, ciki har da mata uku da yaro daya, sanadiyyar rokoki da aka harba cikin Isra’ila a ranar Talata da kuma safiyar Laraba.

Lamarin har ila yau ya jikkata wasu da dama kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

XS
SM
MD
LG