Harin da aka kai kan tungar ta T4, a tsakiyar lardin Homs na zuwa ne sa’o’I bayan da Isra’ilan ta kai wani farmaki a Golan Height dake kudancin Syria.
Isra’ila bata yi wani bayani game da harin a kan tungar sojojin ba, amma dai tace harin da ta kai a Golan martani ne ga rokar da aka harbor mata a ranar Asabar daga Syria.
Firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fada a jiya Lahadi cewa ba zasu lamunta da duk wani makami da za a harba zuwa cikin kasarsu ba.
Cibiyar kare hakkin bil adama ta Syrian Observatory tace farmakin Isra’ila a kan Golan Heights ya kashe mutane goma cikin har da sojojin Syria da ma mayakan kasashen waje.
Facebook Forum