Firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce zai nemi majalisar dokoki ta bashi kariya daga gurfanar da shi gaban shari’a akan zargin cin hanci da rashawa, matakin da ka iya hana yi masa shari’a har sai bayan zaben watan Maris.
Netanyahu ya fuskanci zarge-zarge da dama, ciki har da zargin karban manyan kyautuka da kuma yin alfarma a harkokin siyasa domin bada labarai masu dadi a kansa.
Yana dai bayyana kansa da wanda ake yi masa bita da kullin siyasa.
Ina da niyar neman kariya saboda ina sadaukar da rayuwata domin ku mutane Isra’ila, inji Netanyahu a wani jawabinsa na telabijin a jiya Laraba. Yace amma akwai mutane da basu kaunata sun aikata manyan laifuka kuma suna da kariya har tsawon ransu. Yace wadannan mutane ‘yan lelen kafafen yada labarai ne ‘yan kuma bangaren hagu.
Wani kwamitin majalisar dokoki ne zai yanke shawarar gabatar da batun bada kariyar ga majalisar baki daya domin kada kuri’a a kai, amma babu wannan kwamiti saboda babu gwamnati a yanzu. Ba za a iya shari’a a kan zargin rashawar ba har sai an kammala batun bada kariyar.
Facebook Forum