INEC: A Karon Farko Mace Ta Zama Shugabar Rikon Hukumar Zabe

INEC

Shugaba Muhammad Buhari ya bayar da sanarwar nada Hajiya Amina Bala Zakari a matsayin shugabar rikon hukumar zaben Najeriya ta INEC. Wannan shi ne karon farko da mace zata taba rike hukumar a matsayin shugaba.

Shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya Danladi Kifas ta bakin daraktan sadarwa Haruna Imrana shi ya sanarda Hajiya Amina Bala Zakari cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya bata rikon shugabancin hukumar ta INEC.

Hajiya Amina Zakari wadda ta karanta ililmin magunguna a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria da ta kammala a shekarar 1980. Ita 'yar asalin jihar Jigawa ce. Tayi karatun sakandare a sananniyar makarantar sakandare ta 'yan mata dake Legas da ake kira Queens College.

Bayan ta kammala aikin bautan kasa na shekara daya da duk masu digirin farko ke yi a Najeriya ta yi aiki a wurare daban daban da suka hada da FCT daga shekarar 1983 zuwa 1996 a Abuja. Ta kuma yi aiki da gwamnatin Obasanjo kafin ta zama kwamishana a hukumar zabe.

Biyo bayan nadin da shugaban kasa ya yi mata Hajiya Amina ta kuduri aniyar cigaba da aikin Farfasa Attahiru Jega wanda ya cika wa'adin aikinsa a karshen watan jiya. Tace zata dora kan nasarorin da aka samu lokacin Farfasa Jega. Ta roki Ubangiji Allah ya taimaketa ya yi mata jagoranci.

Lokacin da Farfasa Jega ya cika wa'adinsa ya mikawa Alhaji Ahmed Wali jagorancin hukumar wanda ya rike na kwana daya kafin a nada Hajiya Amina. Alhaji Wali wanda shi ma zai yi ritaya watan gobe ya tabbatarwa Hajiya Amina cikakken goyon bayansa. Yace zai bada hadin kai domin inganta dimokradiya.