Hukumar zaben Nijar CENI tace bata karkata sakamakon zabe ba

Jamhuriyar Nijar: Madam Bayard ta hukumar zaben Nijar wato CENI

Biyo bayan zarge-zargen da 'yan adawa su keyi dangane da sakamakon zaben kasar ta Nijar hukumar zabe CENI tace ta yi ikinta a fili kowa ya gani babu abnu da ta canza.

Dangane da zarge-zargen da 'yan adawa suke yiwa hukumar zaben kasar Nijar da ake kira CENI akan sakamakon da ta bayyana , a karon farko hukumar ta bakin mataimakiyar shugabanta Hajiya Maryama Katambe tace ta hada sakamakon da ake aiko mata a fili babu abun da ta canza.

Hajiya Maryama Katambe tace abun da ya zo gabansu suke bayyanawa al'umma babu kari babu ragewa. Sakamakon da ta samu take aikawa kotun koli wadda ita ce zata yi bincike ta yanke matsayi. Tace idan akwai wani da yake da shakka sai ya mika kukansa ga kotun.

Bisa ga duka alamu shawarar da 'yan adawa suka yanke na kauracewa zaben zagaye na biyu a 20 ga watan Maris ya soma tasiri kan tsare-tsaren zaben. Jiya dole hukumar zaben ta dage taron tantance hotunan 'yan takaran saboda rashin halartar wakilin 'yan adawa. Kuma har yanzu CENI bata bada ranar sake yin aikin ba.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar zaben Nijar CENI tace bata karkata sakamakon zabe ba - 1' 36"