Hukumar zaben kasar ta sanar jiya Laraba cewa, shugaban kasar yana da kimanin kashi 37 cikin dari na kuri’un. Dan takarar hamayya Hamma Amadou yana biye a matsayi na biyu da kashe 22 cikin dari, sai Syni Oumarou da kashi 14%.
Sakamakon ya hada da kuri’un mazabu tamanin da biyu daga cikin dari uku da takwas dake kasar ta yammacin Afrika.
Ranar Talata, gamayyar jam’iyun hamayya tayi watsi da sakamakon zaben da hukumomi suka bayar bisa hujjar cewa, an tafka magudi. Shugaban gamayyar hamayyar Amadou Cisse, yace gwamnati ta kirkiro da dubban mazabu domin murda sakamakon zaben.
Shugaba Issoufou yana neman wa’adin mulki na biyu na shekaru biyar inda ya yi alkawarin murkushe mayakan Islama masu tsats-tsauran ra’ayi da kuma bunkasa kasar da ta kasance daya daga cikin wadanda suka fi talauci a duniya.