Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Nijar sai an yi zagaye na biyu


Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou wanda ya yi ikirarin samun zarcewa a zagayen farko
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou wanda ya yi ikirarin samun zarcewa a zagayen farko

Bisa alamu babu wani dan takara a zaben Nijar da ya ci kujerar shugaban kasa kai tsaye a zagayen farko.

Labarin da muka samu daga kasar Nijar na nuni da cewa sai an yi zagaye na biyu a zaben kasar kafin a tabbatar da shugaban kasa.

A zagayen farko da aka yi ranar Lahadi da ta gabata shugaban kasar mai ci yanzu wanda ya yi ikirarin zarcewa a zagayen farko bai kai labari gida ba domin bai samu kashi hamsin na kuri'un da aka kada ba kamar yadda kundun tsarin mulkin kasar ya tanada.

Yanzu dai sai asa ido a gani wace rana hukumar zaben kasar zata tsayar domin gudanar da zaben zagaye na biyu wanda shi ne zai fitar da shugaban kasa.

Hamma Ahmadu na jam'iyyar MODEN Lumana wanda har yanzu yana kurkuku shi ne kuma ya zo na biyu a wannan zgayen farkon mai 'yan takara goma sha biyar

Hamma Ahmadu na jam'iyyar MODEN Lumana kodayae yana kurkuku shi ne ya zo na biyu a zaben zagayen farko
Hamma Ahmadu na jam'iyyar MODEN Lumana kodayae yana kurkuku shi ne ya zo na biyu a zaben zagayen farko

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG