Gamayyar jam'iyun hamayya a jamhuriyar Nijar, da ake kira (KOPA) a takaice, ta bayyana cewa daga yau dan takarar shugaban kasa Hamma Amadou, wanda ahalin yanzu yake gidan fursina, shine mutumin da zasu goyi bayansa a zaben fidda gwani da za'a yi cikin watan Maris.
Wannan mataki ya biyo bayan sakamakon zaben kasar da aka bayyan ranar jumma'a, wanda ya nuna tilas sai anje zagaye na biyu. Sabanin ikirarin da shugaban kasa mai ci Muhammadu Isouffe yayi, wanda shi da magoaya bayansa suka ayyana cewa, zasu lashe zaben tun a zagaye na farko.
Da yake magana kan sakamakon zaben na ranar Lahadi data gabata, dan majalisar dokokin kasar, kuma dan jam'iyyar hamayya ta Moden Fa Lumana, Bukar Sedu, yace, suna da rahotanni cewa, an tafka magudi a zaben, inda aka si katunan zabe kan kudi jaka 15 na Nijar, watau kimanin Dalar Amurka $30.
Sedu yace, a wasu wuraren, an kwace katunan zaben mata baki daya, aka hana su zabe sai maza kadai suka yi zabe.
Shugaban jam'iyyar RDP zumunci- Alhaji Yusuf Bashar, shine ya bayyana matakin 'yan hamayya na tsaida Hamma Amadou, a zaman dan takararsu.
Ga karin bayani.