Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zabe ya gudana cikin lumana a Nijar amma da korafi


Jamhuriyar Nijar: Madam Bayard ta hukumar zabe
Jamhuriyar Nijar: Madam Bayard ta hukumar zabe

An yi zabe an gama cikin kwanciyar hankali da lumana a jamhuriyar Nijar jama'a kuma sun yi hamdala ga Ubangiji da aka yi zaben aka kuma kare ba tare da wata matsala ba

To saidai shugaban jam'iyyar MNRD Hakuri, Muhammad Usman ya koka da cewar a wasu wurare an samu matsaloli har ma ana sayen kuri'u.

Muhammad Usman yace yana fadan abun da ya samu hakikanci akansa ne. Kuri'un wasu 'yan takara basu isa wani wuri ba. Wasu kuma sun isa amma ba isassu ba.Akwai kuma sayen kuri'u.

Inji Muhammad Usman yace kuri'un jam'iyyarsa an sasu kasuwa. Ana tare masu zuwa rumfunan zabe ana sayen kuri'un.

A wani halin kuma Bukari Sani Zilli na jam'iyyar PNDS Tarayya ya mayar da martani inda yace mutane yakamata su yi aiki da dimokradiya da doka. Bayan an rufe kemfen har ranar zabe 'yan adawa suna tsaye suna kemfen. Wai suna tare mata da matasa suna gaya masu jam'iyyar da zasu jefawa. Yace sun kuma san sanu daba daladala daridari domin a jefa masu kuri'u.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG