Kotun tsarin mulki mai matsayin kotun shari'ar zabe ta dauki matakan soke zabe a wasu mazabu masu tarin yawa yawa dake kasar Ghana bayan la'akari da ta yi da wasu kurakurai da tace sun dabaibaye ayyukan kada kuri'a.
Kotun ta kuma ci gyara wasu kurakuran na daban da aka samu cikin wasu rassan hukumar zabe a wasu wuraren zabe a jamhuriyar Nijar inda ta ce an birkita kuri'un wasu 'yan takarar shugaban kasa da wasu takwarorinsu.
Sakamakon da kotun ta bayar ya kara jaddada Shugaban kasa Mahammadou Issoufou na PNDS a matsayin wanda yake kan gaban 'yan takara 15 da suka gwafza a zaben ranar 21 ga watan jiya..Kotun tace ya samu kashi 48.43 maimakon kashi 48.41 wanda hukumar zabe ta bayar can baya. Har yanzu Hamma Ahmadou ke bin Issoufou da kashi 17. 73 maimakon 17. 79 da hukumar zabe ta fada.
Kotun ya tabbatar babu dan takara da ya samu kashin hamsin na kuri'un da aka kada ke nan dole ne a je zagaye na biyu na zaben. Kotun ta tabbar cewa Mahammadou Issoufou da Hamma Ahmadou ne zasu sake karawa a zagaye na biyu a ranar 20 ga wannan watan.
Bayyana sakamakon zaben da kotun ta yi ya ba 'yan siyasa soma fafutikar neman zabe daga daren jiya Litinin. Majalisar ministoci ta bada sanarwar sakin ragama ga 'yan takara cewa su fara zagaye yankunan kasar domin neman kuri'u.
Ga karin bayani.