Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon farko farko zaben Nijar sun nuna Mahammdou Issoufou ke kan gaba


Shugaba Mahammadou Issoufou
Shugaba Mahammadou Issoufou

A Nijar sakamakon farko farko na zaben shugaban kasa, ya nuna shugaba Muhammadou Issoufou yana kan gaba, amma tuni 'yan hamayya suka yi watsi da sakamakon zaben.

Sakamakon kidayar da hukumar zaben kasar ta bayyana a safiyar yau Talata, ya nuna shugaba Isouffou yana kan gaba da kimanin kashi 40 cikin dari na kuri'un da aka kada, yayinda dan hamayya Hama Amadou yana da kashi 29 cikin dari, sai kuma Seyni Oumaru yana da kashi 12 cikin dari.

Sakamakon zaben ya shafi gundumomin zabe 20 ne daga cikin gundumomi 308 na kasar.

Gamayyar jam'iyun hamayya tuni ta yi watsi da sakamakon da cewa magudi ne aka yi. Shugaban gamayyar ta 'yan hamayya, Amdou Cisse, ya fada yau talata cewa, gwamnati ta kafa "dubban rumfunan zabe na karya"domin ta murda sakamakon zaben.

Shugaba Muhammadu Isouffou, yana neman wa'adi na biyu wasu shekaru biyar, tareda alkawarin zai murkushe mayakan sakai masu ikirarin musulunci, sannan ya habaka kasar Nijar, wacce take cikin jerin kasashe mafiya talauci.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG