Lamarin ya kai har ana yi masu zargi kala-kala na cewa kila niyyarsu ta kabilanci ce ko kuma su sa wasu su fi wasu samun mazabu da kuri'u.
Sabili da neman wanke kansu yasa shugaban ya kira taron manema labarai domin ya bada cikakken bayani dangane da manufarsu wurin kirkiro sabbin mazabu.
Mazabun da ake dasu yanzu an kirkirosu ne tun 1996 lokacinda yawan 'yan Najeriya bai wuce miliyan 110 ba amma a yanzu haka kidigdiga da hukumar dake nazarin yawan jama'ar kasar, yawan 'yan kasa ya kai miliyan 175 wato kimamnin karin mutane miliyan 65 ke nan. Dalili ke nan idan an zo yin zabe sai a ga mazaba nada mutane dubu hudu, ko uku. Amma bisa ga tsari bai cancanta a ce mazaba ta fi mutum dari biyar ba. Idan mazaba tana da mutane dari biyar to komi zai zo da sauki.
Yawan jama'a yasa hukumar ta gani cewa ya dace ta kirkiro sabbin mazabu kafin a yi zaben 2015. Haka ma wasu sabbin unguwannai sun taso. Misali Legas, Abuja, Onitsha ko Kaduna a 1996 da aka kirkiro mazabun babu wadannan unguwannin. Amma ga unuguwannin amma ba mazabu. Don haka idan har ana son mutane su fito su yi zabe cikin walwala to dole ne sai an kara mazabu.
A kowace jiha hukumar tana da rajistan mutane da suka yi rajista wadda an tantanceta an cire sunayen wadanda suka yi rajista fiye da sau daya. To sai a raba jimilrar sunayen da dari biyar domin su san iyakacin mazabun da kowace jiha ya kamata ta samu. Daga nan zasu yi nazarin yadda za'a kara mazabun domin a samu walwala.
Abun mamaki sai wasu suna cewa ai nufin kirkiro mazabun domin a kyautata wa wasu ne a kuma kuntatawa wasu. Shugaban yace ainihin gaskiya ba haka ba ne.
Ga cikakken rahoto.
Your browser doesn’t support HTML5