Tun farko shugaban hukumar zaben Najeriya ta INEC ya ja kunnen mutane game da daukan hotunan kuri'un zabe da takardun da akwatin zabe a lokacin zaben gwamna da za'a yi gobe. Yin hakan karya doka ne kuma duk wanda yayi hakan za'a hukuntashi.
Wannan umurnin ne gwamnan jihar Osun Rauf Argbesola ya kira jama'ar jihar su bujurewa. Gwamnan na jihar ta Osun yayi kiran ne a wajen yakin neman zaben gwamna inda yake neman zagaye na biyu. Gwamnan dan jam'iyyar APC yayi furucinsa ne a dandalin Nelson Mandela dake tsakiyar birnin Osogbo fadar gwamnatin jihar.
Gwamnan yace duk wanda yake da yawar salula mai daukan hoto ya riketa ya dauki hoton kuri'a da akwatin kada zabe ya kuma rubuta lambar kuri'arsa. Gwamnan yace ba zasu sake bari a tabka irin magudin da aka tafka a jihar Ekiti ba a jihar Osun. Yace babu dokar da ta hana a dauki hoto.
Idan ba'a manta ba shugaban hukumar zabe ta INEC Farfasa Attahiru Jega a wani taron masu ruwa da tsaki dangane da zaben gwamnan Osun yace umurnin da gwamnan Osun ya bayar cewa a dauki hoton katin zabe da akwatin zabe da rubuta lambobin katin zabe sun sabawa dokar zabe. Yace kuma duk wanda ya sabawa dokar idan an kama shi zai yi zaman gidan maza na watanni shida ko ya biya tarar nera dubu dari.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.