Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zabe Tace Bata da Masaniya Akan Tsige Gwamnan Adamawa


Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega
Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega

An soma mayar da martani akan kalamun shugaban hukumar zabe ko INEC Farfasa Attahiru Jega wanda yace ba'a sanar da hukumar ba tsigewar gwamnan jihar Murtala Nyako da majalisar jihar ta aikata.

Bisa ga doka akan gudanar da zaben cike gurbi ne cikin wata uku da zarar an tsige gwamna.

Kalamun shugaban hukumar zaben ya soma jawo martani. Ibrahim Bappa Waziri wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Adamawa yace kalamun shugaban hukumar zaben nada ayar tambaya. Yace yakamata hukumar ta yiwa kanta adalci domin ta gani a talibijan yadda aka rantsar da mukaddashin gwamna. Ta karanta a jaridu yadda aka tsige gwamnan. Shin wanene kuma hukumar take so ya sanar da ita, kuma wane irin sanarwa. Yace yana ganin shi mukaddashin gwamnan ne yake neman a barshi ya karasa watanni goma sha daya da suka ragewa Murtala Nyako ya kammala wa'adin mulkinsa. Yin hakan kuma haramtacen abu ne.

Bappa Waziri ya cigaba da cewa ba zasu yadda ba. Zasu fito kwansu da kwakwatarsu su yi zanga zanga su tabbatar an gudanar da zabe cikin wa'addin da doka ta tanada. Haka ma masana shari'a sun ce zasu kalubali duk wani yunkurin hana zaben cike gurbin. Kamata yayi majalisa ta rubutawa INEC abun da tayi kana shi mukaddashin gwamnan ya rubutawa hukumar zabe (INEC) cewa babu zababben gwamna a jihar.

Sai dai tuni wasu 'yan takara suka soma daura damarar shiga zaben cike gurbin. Shugabar mata ta jam'iyyar APC tace duk da sun kalubali tsige gwamnan a kotu a shirye suke su tsayar da dan takara a zaben cike gurbin.

Yayin da ake wannan dambarwar wasu kungiyoyi sun fito suna neman mukaddashin gwamnan Ahmed Umar Fintiri da ya zarce.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG