Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jonathan Ya Sake Nanata Yin Adalci a Zaben 2015


Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan

A zabe mai zuwa shugaba Jonathan yace yakamata kowace kuri'a tayi tasiri domin biyan bukatun masu kada kuri'un.

Shugaba Jonathan ya kara nanata alkawarin yin adalci a zaben 2015.

Shugaba Jonathan wanda mukarrabansa suka ce zai sake tsayawa takara yace gwamnatinsa zata sa tsarin zaben ya zama mai ban sha'awa. Yace zai tabbatar cewa hukumar zabe ta samu isasshen kudi ta kuma zama mai cin gashin kanta.

Amma mafi yawa dake goyon bayan Janaral Buhari suna dari-dari da akawarin shugaban yayin da suka ce idan har za'a yi zabe mai adalci sai an ba hukumar zabe isasshen kudi, cusa sabbin jami'ai domin hukumar ta zama mai cin gashin kanta. Kazalika jami'an tsaro su gujewa son zuciya.

A nasa bangaren shugaban zaben Farfasa Attahiru Jega ya nesanta hukumar da zargin da ake yi mata cewa tana tallafawa wurin tafka magudin zabe. Yace abun da suka fahimmata mafi yawan 'yan bautan kasa da suke aikin zabe wasu tsoratasu ake yi su yi magudin zabe. Zaben da ya fi muni shi ne na Gaya a jihar Kano. Babu abun da ba'a yi ba a zaben. An kawo 'yandaba, makamai, an tarasu kusan kwana uku kafin zabe. Farfasa Jega yace tabargazar da aka yi shi bai taba ganin irinta ba.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG