Shugaban Hukumar Zabe ko INEC Farfasa Attahiru Jega shi yayi kiran yayin da yake zantawa da wakilan kafofin labaran kasashen ketare akan babban zaben da za'a yi a watan Faburairun badi.
Yace wasu masu kada kuri'a sun ga laifinsa domin rashin fahimtar doka da jajircewa da yayi domin bin ka'ida. Yace hukumar zata yi anfani da wata naura mai samfarin salula domin tantance masu kada kuri'a a zaben na 2015 domin gujewa magudi.
Farfasa Attahiru Jega yace da an shafa naurar zata fitar da suna da hoto, idan kuma mutum ya sa yatsarsa naurar zata fada kuma duk wanda yake wurin zai ji. Idan an tantance mutum ko ba'a yi ba duk zata fada. Abun da yasa suka yi haka abun yayi zafi. Katunan zaben ma sayewa su keyi kana ranar zabe sai su ba wani ya zo yayi zabe da ita. Da ikon Allah a zaben 2015 ko sun sayi katin ba zasu iya anfani da shi ba sai dai idan sun zo da wanda ya sayar masu da katin ya zo ya kuma zabesu da kansa.
Akan tsarin a kasa a tsare yace halal ne matuka idan tsarin ba zai kawo fitina ba. Yace amma shi ba mai sihiri ko gani har hanji ba ne wajen gano duk kumbiya-kumbiyar da za'a tafka ranar zabe. Akan karbe zabukan kananan hukumomi Farfasa Jega yace idan an yi hakan hukumar zata yi na'am.
Shugaban ma'aikatan kananan hukumomi Ibrahim Khalil yace sai manyan masu rike da kujerun siyasa da jami'an tsaro sun kaucewa son rai ne kawai za'a iya gyara dimokradiyar Najeriya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.