Dansandan yace sun yi wata shida suna aiki amma sai kwana kwanan nan aka basu kudin wata daya kuma nera dubu goma sha biyar kawai.
Gwamnatin PDP yace bata kula da jami'an tsaro ba. Suna son a canza mulki watakila sabuwar gwamnati ta kayutatawa jami'an tsaro.
Bayan ikirarin dansandan 'yan adawar APC na farin ciki da sakamakon zaben jihar Osun wanda tamkar tsallake siradin rasa karin jiha ne bayan da jam'iyyar ta rasa jihohin Ekiti da Adamawa.
Kakakin PDP ya fito ya yabawa Shugaba Jonathan inda yace nuna adalcinsa ne ya sa APC ta samu jihar Osun din. Ya caccaki 'yan adawa da neman tada zaune tsaye har ma da kokarin tursasa jami'an tsaro.
Barrister Abdullahi Jalo mataimakin kakakin jam'iyyar PDP yace suna jira su samu sakamakon zaben daga kananan hukumomi , su karanta kana su dauki matsayin PDP. PDP zata yi nazarin rashin nasarar dan takararta Sanata Omisore inji Yarima Muri. Yace bai nuna dole sai PDP ta ci ba amma sun fi so su ci. Zasu koma su dubi inda suka yi kuskure saboda zabubbuka masu zuwa. Yace duk lokacin da shugaban kasa da mataimakinsa suka yi magana sun ce za'a yi zabe cikin adalci kuma kowa ya ci za'a bashi.
Shugaban hukumar zabe Farfasa Attahiru Jega yace sun yi adalci. Ya ce ai dama ba'a firgitashi domin a yi magudi. Irin hali nasu na Najeriya ana ganin mai mulki zai iya komi kuma a can baya sun yi komin. Sabili da haka ana ganin babu abun da ya canza amma tun da ya zama shugaban hukumar ba'a taba tafka magudi ba ko yin murdiya ba.
To saidai zaben shekarar 2015 shi ne zai nuna ko adawa zata iya amshe ragamar mulki daga PDP kodayake kayar da jam'iyya mai mulki abu ne mai wuya. To saidai a yammacin Afirka adawa tayi nasara a kasashen Niger, Ghana da Ivory Coast.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.