Kwamishanan hukumar zaben na jihar Adamawa yace tsaikon da aka samu wajen fitar da ranar zaben ya samo asali ne sakamakon rashin sanar da hukumar akan kari da majalisar dokokin jihar Adamawan tayi.
Inji kwamishanan yanzu hukumar zaben ta kammala duk wasu shirye-shiryen da suka kamata akan zaben. Kamar yadda suka yi taro a Abuja shugaban hukumar Farfasa Attahiru Jega yace ranar Juma'an nan za'a bayar da sanarwar zaben a hukumance bisa ga ka'idar da kundun tsarin mulki ya shirya. Daga lokacin sanarwar zuwa bakwai ga wata mai zuwa yakamata a ce jam'iyyun siysa sun kammala fitar da 'yan takaransu.
Amma tuni jam'iyyu suka fara daura damarar shiga zaben cika gurbin. Shugabar APC ta jihar Binta Mato tace duk da cewa suna kotu suna kalubalantar tsige gwamna Murtala Nyako zasu shiga zaben. Tace an cire masu gwamna ne ba akan ka'idar da doka ta shimfida ba.
Magoya bayan mukaddashin gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri tuni suka fito suna neman shi ma ya shiga takarar, wato yayi tazarce domin ya kammala wa'adin mulkin gwamna Nyako. Wani Oanarebul Tudun Maduwa na cikin masu irin wanna ra'ayin. Yace Fintiri dan Najeriya ne kuma dan jihar Adamawa ne. Yana da 'yancin ya tsaya zabe. Koda ma ya ki ya tsaya zaben talakawan Adamawa zasu tilasta masa.
Amma maukaddashin gwamnan yace shi bai yi magana ba kuma bai yi shawara da kowa ba. Wai idan sun kawo "bakin gada zasu san yadda zasu tallka". Yace yanzu lokacin bai zo ba. A wani hannun kuma an ce wasu tsofofin 'yan jam'iyyar PDP tuni suka janyewa tsohon shugaban hukumar EFCC Malam Nuhu Ribadu.
Ga rahoton Ibrahin Abdulaziz.