Hukumar Kula Da Alkalumman Ci Gaban Kasa Ta Bada RahotoNn Durkushewar Tattalin Arzikin Najeriya

Hukumar kula da alkalumman ci gaban kasa a Najeriya ta bada wani rahoto wanda ke nuna cewar tattalin arzikin Najeriya ya durkushe kuma yana fuskantar babban kalubale, ganin yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi, da kuma durkushewar kudin shiga wanda ya shafi bangarori daban daban na jama’a da kuma kasar baki daya.

Wannan sharhi da hukumar ta fitar a yau, ya nuna a zahiri cewa tattalin arzikin Najeriya na matukar ci gaba da durkushewa kuma matsalolin daban daban da kasar ke fuskanta saboda karyewar farashin man Fetur, da kuma karayar darajar Naira idan aka kwatantata da kudin ketare.

Alhaji Sani Aminu, kwararre ne akan sha’anin tattalin arziki kuma yayiwa wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Umar Faruk Musa, bayanin cewa kamata yayi masu sharhin su mayar da hanakli akan abubuwan da kasa take wallafawa ko samarwa domin ta haka ne kawai za’a kwantarwa da jama’a hankali kuma su san inda aka dosa.

Haka kuma da ya zanta da ministar kasafin kudi da tsare tsare ta Najeriya Hajiya Zainab Ahmed, ta bayyana cewa da suka duba wannan rahoto sun fahinci cewa duk da has ashen da asusun bada lamuni na duniya yayi na cewa “tattalin arzikin zai sauka, hakan ta faru amma ba kamar yadda asusun ya zayyana ba, wato Kenan abubuwan basu baci kamar yadda asusun yayi bayani ba.

Rahoton ya bayyana cewa akwai abubuwa da dama da suka gyaru, kuma kowa yasan daman gyara sai a hanakali, kuma jarin da ya shigo cikin watanni shida ya fi jarin da ya shigo kasar a shekarun baya.”

Saurari cikakken rahoton Umar Faruk Musa, a nan.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kula Da Alkalumman Ci Gaban Kasa Ta Bada RahotoNn Durkushewar Tattalin Arzikin Najeriya