Gwamnan jihar Hon, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira domin shaidawa duniya irin halin da ake ciki a jihar ta Borno, musamman yadda kudaden suke bacewa cikin albashi.
Gwamnan ya bayyana cewa akwai kiyasin ma’aikata dubu ashirin da biyar ne a fadin jihar, kuma yanzu haka an tantance mutane dubu goma sha daya da tasa’in da bakwai wadanda basu da wata matsala, sai dai ya kara da cewa mutane dubu goma da dari bakwai da sittin da uku ne suka halarci tantancewar a cikin adadin duka ma’aikatan jihar, amma har yanzu ba’a sami damar kammala tantance sub a sakamakon wasu matsaloli da suke fuskanta.
Hon, Kashim ya ci gaba da cewa wadanda aka kammala tantancewar kuma aka tabbatar ma’aikata ne na kwarai, kudaden su na watanni biyu sun kama Naira Biliyan daya da miliyan Dari da ashirin da tara, da dubu dari uku da ashirinne kacal, yayin da aka sami rarar wasu kudaden. Ta dalilin haka ne gwamnan ya bada umurnin a cigaba da biyan wadanda aka tantance kuma aka tabbatar basu da wata matsala.
Ya ce, yanzu haka akwai mutane dubu bakwai da dari uku da tasa’in da biyu da ba’a riga an tantance su ba a sakamakon matsaloli da suke fuskanta, kama daga matsala tsakaninsu da bankunan su, da matsalolin daukar aiki ba bisa doka ba, da kuma masu takardun bogi, dan haka sai an kammala tantance wadannan mutane kafin a biya su al’bashin su.
Gwamnan ya bayyana cewa a shirye yake ya tari duk wani abu da ka iya tasowa a matsayinsa na shugaba, domin kuwa a cewar sa, yana da labarin cewa wasu na shirin gudanar da zanga zanga akan matakin da gwamnatin jihar ta dauka, wasu kuma na shirin afkawa wurin da ake gudanar da tantancewar, wasu ma cewa suke zasu sawa sakateriyar jihar wuta.
Daga karshe gwamnan ya jawo hankulan bankunan dake jihar da su guji hadin baki da irin wadannan mutane, domin sun gano cewa jama’a kan bude asusun ajiya domin albashi ya rika shiga kai tsaye.
Domin Karin bayani ga rahoton Haruna Dauda Biu.