Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasa Da Albarkatun Man Fetur Sun Durkusar Da Manyan Kasashen Afirka Biyu


Siyasa da kuma albarkatun man fetur sun durkusar da manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika, Afrika ta Kudu da kuma Najeriya, yayin da kasashen biyu suke fuskantar komadar tattalin arziki.

Yau Laraba Najeriya, kasar da tafi kowacce arzikin man fetir a nahiyar, zata fitar da rahotonta na kwata-kwata, da mai yiwuwa zai tabbatar da fadawar kasar komadar tattalin arziki. Yayin da Afrika ta Kudu, kasar da tafi kowacce tsari da zaunannen tattalin arziki, ke fuskantar koma baya, inda tattalin arzikin kasar ya fadi da kashi daya da digo biyu cikin dari a kwatar farko, yayin da yawan al’ummar kasar ke kara habaka fiye da tattalin arzikin kasar. Ana kyautata zaton gwamnatin kasar zata fitar da nata rahoton kwata ta biyu mako mai zuwa.

Kasashen biyu suna gajin juna a matsayin abokan gasa. A cikin shekarun baya bayan nan, kasashen sunyi kokarin shan gaban juna a zama kasar da tafi karfin tattalin arziki a nahiyar, inda kwanan nan Najeriya ta rasa matsayin ga Afrika ta Kudu. Sai dai masu zuba jari na kasa da kasa suna daukar kasashen a matsayin jirgi daya, bisa ga cewar Martyn Davies darektan kasuwanni masu tasowa da hulda da Afrika.

Faduwar farashin danyen mai a kasuwannin kasashen duniya ya gurguntar da tattalin arzikin Najeriya. Banda kuma hare haren da mayaka suke kaiwa a yankin Naija Delta da ya sa man da ake haka ya ragu zuwa kimanin gangan miliyan daya da dubu dari biyar a rana daga miliyan biyu da dubu dari biyu.

Wata matsalar da Najeriya ke fuskanta kuma ita ce karancin kudaden kasashen waje, wanda ke nufin karancin kayan aiki da masana’antu ke shigowa dasu daga kasashen ketare, da kuma kayan da ake sayarwa a kasuwanni. Wannan yana haifar da hauhawar farashin kayayyaki.

Tattalin arzikin Najeriya ya sami koma baya da kimanin digo hudu cikin dari a kwatar farko, ana kuma kyautata zaton lamarin zai kara muni a kwata ta biyu. Wani kwararre a fannin tattalin arziki a birnin London, John Ashbourne yace, yana sa zuciya tattalin arzikin Najeriya zai fadi da kashi uku cikin dari, amma yana tsammanin zai fara farfadowa badi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG