Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Bankin Najeriya Zai Tsayawa Manoma Don Samun Lamani Daga Bankuna


Kayayyakin noma zuben a hedkwatan ma’aikatan aikin gonar jihar, Borno a Maiduguri, 26, ga Mayu 2014.
Kayayyakin noma zuben a hedkwatan ma’aikatan aikin gonar jihar, Borno a Maiduguri, 26, ga Mayu 2014.

Babban bankin Najeriya zai tsayawa manoma don samun lamanin Noma da zai kai ga tarawa da sayarwa manoma amfanin gonar bayan komai ya kammala.

Banki dai ta hanyar wata cibiyarsa mai suna NIRSAL a takaice, zai tsayawa manoman ne don samun lamani daga bankuna da hakan zai sanya samun taki da iri da kuma injinan ban ruwa ga manoman rani da sauran kayan aiki.

Babban manajan shirin Aliyu Abdulhamid Abbati, yace aikinsu ne su dauki takardun manoma su kaiwa bankuna domin samar musu da bashin da suke bukata. Ya kuma kara da cewa Najeriya zata iya ciyar da kanta ba tare da an shigo da abinci ba daga kasashen waje.

Gwamnatin Najeriya dai ta zuwa Naira Biliyan Saba’in da Biyar ga shirin NIRSAL, don samun karfin jarin lamuntar manoman a bankuna.

Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG