Bayan da hamshakin 'dan kasuwan Najeriya, Aliko Dangote, ya gayyace shi ya ziyarci wani sansanin da aka tsugunar da kimanin ‘yan gudun hijira na cikin gida miliyan biyu da dubu dari uku a Arewa maso Gabashin Najeriya, inda hare haren kungiyar Boko Haram yafi shafa. Dan fafatukar kare hakkokin bil’adama ya yi bayani mai sosa rai a taron manema labarai a Abuja.
Yace “mun sani kananan yara dubu hamsin zasu mutu kafin karshen wannan shekarar, bisa ga cewar MDD, idan basu sami tallafin dala miliyan dari uku da suke bukata ba. A halin yanzu sun sami miliyan dari daya kadai. Saboda haka abinda aka samu, cikin cokali ne na abinda ake bukata.”
Ko da shike rundunar sojin Najeriya ta sami ci gaba a fannin yaki da kungiyar Boko Haram, yace, ana bukatar kudi domin sake gina yankin. Yace babu gidajen da mutanen da suka rasa matsugunansu zasu koma, an kona garuruwansu da kauyukansu. Kun san da haka, ni ban sani ba.
Bono ya yi alkawarin amfani da matsayinsa wajen neman tallafin kudi, da kuma sake komawa yankin ya taimaka. Yace babu isasshen lokaci kuma bukatun suna da yawa.