A cigaba da gudanar da bincike akan tsoffin jami'an gwamnatin Najeriya da suka yi sama da fadi da dukiyar kasar, hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC a takaice, tace bata da maaniya an janje canjin da ake yiwa tsohuwar ministan mai Diezani Madueke.
Ita dai Diezani Madueke har yanzu tana London. Tun watan jiya manyan jaridun Najeriya suka ruwaito EFCC ta janye karar da ta shigar ta tuhumar Diezani ta hanyar lauyanta Rotimi Jacob.
Kazalika ita EFCC din bata tabbatar da sace dalar Amurka biliyan daya ta hanyar babban banki ba.Kakakin hukumar yace ba zai ce komi akan lamarin ba.
Wasu masu mara baya ga yaki da cin hanci da rashawa suna ganin takaita binciken da EFCC keyi kan gwamnatin da ta shude shi ya fi a'ala saboda fadadashi zai bata lokaci. Sun ce bankado wata badakala a lokacin mulkin soja zai janyo dawainiya mai yawan gaske.
A ra'ayin Muhammad Tajudden wani limami a Abuja yace yin dogon bincike da ya hada da gwamnatocin baya zai sa gwamnatin Buhari ta shagala tare da dauke hankalinta daga abubuwan da suka fi mahimmanci. Amma wajibi ne a binciki wadan da aka karbi gwamnati a hannunsu saboda barnar da suka yiwa kasar.
Amma kungiyoyin irinsu Useni Kumbi suna ganin komi tsawon bincike kamata yayi a cigaba dashi har sai an hukumta duk wadanda suka wawure arzikin kasa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.