Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Osun Ta Shirya Karbar Bakuncin Shugaba Muhammad Buhari


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Gobe Alhamis ake kyautata zaton shugaban Najeriya zai kai ziyara jihar Osun dake kudu maso yammacin kasar, jihar da kwanan nan ta fito daga rikicin sanya hijab a makarantu

A sakamakon ziyarar ta Shugaba Muhammad Buhari zuwa jihar Osun, rundunar 'yansandan jihar tace ta shirya tsaf ta karbi bakuncin shugaban tare da samar da cikakken tsaro a birnin Osogbo babban birnin jihar..

Jami'in hulda da jama'a na rundunar shi ya tabbatarwa Muryar Amurka shirin da suka yi. Yace sun shirya domin yin aiki saboda ziyarar shugaban kasa. Yace babu wani fargaba. Ashirye suke da ayyukan tsaro.

Yace duk matakan tsaron da ya kamata su dauka sun dauka domin samun nasarar ziyarar shugaban..

Tuni wani yankin sojojin Najeriya ya isa birnin Osogbo tare da wasu jami'an tsaro masu sanya kayan sarki da masu shiga farin kaya. Duk wuraren da shugaban zai je a birnin an takaita tafiyar mutane.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:35 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG