Harbe-Harben Bindiga Sun Tarwatsa Shari’ar Zaben Edo

Yan bindiga

Kotun ta fara zaman sauraron korafe-korafen dake kalubalantar zaben da ya gudana a ranar 21 ga Satumban da ya gabata wanda ya ayyana Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Harbe-harben bindiga sun tarwatsa zaman kotun sauraron korafe-korafen zabe ta Edo wacce ta fara zamanta a yau Laraba a birnin Benin, fadar gwamnatin jihar.

An bada rahoton cewa an hangi batagari a wajen kotun inda karar harbin bindiga ta sanya mutane gudun neman tsira.

Kotun ta fara zaman sauraron korafe-korafen da ke kalubalantar zaben da ya gudana a ranar 21 ga Satumban da ya gabata wanda ya ayyana Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Babban mai kalubalanta a kotun shi ne Asue Ighodalo na jam’iyyar PDP.

Hukumar zaben Najeriya inec ta ayyana Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 291, 667, inda aka ce Ighadalo na jam’iyyar Pdp ya samu kuri’u 247, 274 yayin da Olumide Akpata na jam’iyyar Lapour yazo a mataki na 3 da kuri’u 22, 763.

Har ila yau, jam’iyyun PDP da APC na ci gaba da musayar yawu dangane da harbe-harben bindigar inda dukkaninsu ke zargin juna da daukar nauyin lamarin.