Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Yi Fatali Da Sakamakon Zaben Jihar Edo


Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP, Ambasada Iliya Damagum (Hoto: Facebook/PDP - Screenshot)
Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP, Ambasada Iliya Damagum (Hoto: Facebook/PDP - Screenshot)

A ranar Lahadi, hukumar INEC ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben jihar ta Edo, nasarar da PDP ta ke kalubalanta.

Jam’iyyar PDP ta yi kira ga Hukumar zabe Mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta sake duba sakamakon zaben gwamnan Jihar Edo.

A ranar Asabar al’umar jihar wacce ke kudu maso kudancin Najeriya suka kada kuri’unsu a zaben.

A ranar Lahadi, hukumar INEC ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sai dai jam’iyyar ta PDP ta nemi INEC da ta sake duba sakamakon tana mai cewa bai nuna asalin yadda al’umar jihar suka kada kuri’unsu ba.

Mukaddashin Shugaban jam’iyyar ta PDP a wani taron manema labarai a Abuja, Ambasada Umar Damagum, ya ce jam’iyyar za ta kalubalanci zaben a kotu.

Damagum ya bayyana cewa mutanen Edo Dr. Asue Ighodalo na jam’iyyar PDP suka zaba a matsayin gwamna na gaba, yana mai cewa dole a bar zabinsu da suka bayyana a rumfunan zabe.

“Za ku iya tunawa cewa PDP ta sha jan hankali kan kitse-kitsen da APC ta yi na ganin ta murde zaben.”

“A dalilin haka, jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben Gwamna na jihar Edo, saboda bai da sahihancin da tsarin dimokradiyya ya tanada.

“PDP na kira ga hukumar zabe ta INEC da ta sake duba sakamakon zaben jihar Edo kamar yadda dokar zabe ta sashe 65 ta shekarar 2022 ta ba ta dama. In ji Damagum.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Najeriya, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba ya garzaya kotu.

“Shugaba Tinubu na kira ga wadanda ba su gamsu da sakamakon zaben ba da su bi ta hanya da doka ta tanada don neman hakkinsu.” Onanuga ya ce.

Okpebholo na APC ya samu kuri’u kuri'u 291,667. Sai dan takarar jam’iyyar PDP Asue Ighodalo wanda ya samu kuri'u 247,655.

Olumide Akpata, na jam'iyyar Labour Party (LP), ya kammala a matsayi na uku, inda ya samu kuri'u 22,763.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG