An rantsar da Monday Okpebholo a matsayin gwamnan jihar edo, al’amarin da ya kawo karshen mulkin Godwin Obaseki bayan ya kammal wa’adi na biyu a kan karagar mulki.
A yau Talata bikin rantsuwar ya gudana a filin wasan Samuel Ogbemudia da ke Birnin Benin, fadar jihar Edo, watanni biyu bayan da jam’iyyar APC ta lashe zaben da aka gudanar a jihar.
Okpebolo yad au rantsuwar kama aiki da mataimakinsa, Dennis Idahosa.
A ranar 22 ga watan Satumban da ya gabata ne hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana Monday Okpebholo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Edo.
Monday Okpebholo ya samu nasara ne a kan abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP mai mulki Asue Ighidalo.
Babban jami'in tattara sakamakon zaben gwamnan Edo Farfesa Faruk Adamu Kuta ya bayyana cewa Monday Opebholo ya samu kuri'u 291,667 yayin da Asue Ighodalo ya samu kuri'u 247,274.
Sakamakon ya nuna cewa jam'iyyar Labour ce ta zo ta uku, inda dan takararta Olumide Akpata ya samu kuri'u 22,763
Dandalin Mu Tattauna