Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Obaseki Ya Ce Kan Sakamakon Zaben Gwamna A Jihar Edo


Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki (Facebook/Godwin Obaseki)
Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki (Facebook/Godwin Obaseki)

A wata sanarwa da ya fitar ta hannu kakakinsa Bayo Onanuga, Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba, ya bi hanyar da doka ta tanada don bin kadi.

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya yi kira ga al’umar jihar da su zamanto masu bin doka da yin da’a yayin da aka fitar sakamakon zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar Asabar.

A ranar Lahadi, hukumar zabe ta INEC ta sanar da Monday Okpebholona na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 291,667.

Sai dan takarar jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo da ya samu kuri’u 247,274 da dan takarar LP, Olumide Akpata da ya samu kuri’u 22,761.

Sai dai Gwamna Obaseki da zai kammala wa’adinsa a watan Nuwamba, ya koka da sakamakon zaben.

“Abin takaici shi ne, ga dukkan alamu, sakamakon zaben gwamna na ranar 21 ga watan Satumba, ya kashewa mutane da dama kwarin gwiwa a jihar Edo duba da yadda hukumomin da ya kamata su kare mutane suka rika gallaza musu.

“Dadin tsarin Dimokradiyya shi ne, yadda yake ba mutane iko zabar wanda zai shugabance su. Saboda haka, idan aka kwace wannan iko daga hannun jama’a, wannan ya wuce abin takaici, kuma shirme ne.” Obaseki ya ce a wani jawabi da ya yi ga al’umar jihar wanda aka wallafa a shafukan sada zumunta a jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben.

Gwamna ya kuma yi kira ga jama’a da su kai zuciya nesa.

“Amma duk da haka, ina mai kira a gare ku, ya ku al’umar jihar Edo da ku kwantar da hankalinku kada ku dauki doka a hannu da bata dukiya duk da wannan takala da aka yi muku.” Obaseki ya kara da cewa.

A wata sanarwa da ya fitar ta hannu kakakinsa Bayo Onanuga, Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba, ya bi hanyar da doka ta tanada don bin kadi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG