Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Edo: Okpebholo Ya Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Gwamnatin Obaseki


Tsohon gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki (Facebook/Godwin Obaseki)
Tsohon gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki (Facebook/Godwin Obaseki)

Kwamitin, da za’a rantsar a gobe Talata 26 ga watan Nuwambar da muke ciki, a fadar gwamnatin jihar dake birnin Benin, zai kasance karkashin jagorancin Dr. Ernest Afolabi Umakhine.

Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya amince da kafa kwamitin tantance kadarorin jihar mai mambobi 14 domin bincikar gwamnatin mutumin daya gabace shi, Godwin Obaseki.

Sakataren yada labaran gwmnan, Fred Itua, ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi.

A cewarsa kwamitin, da za’a rantsar a gobe Talata 26 ga watan Nuwambar da muke ciki, a fadar gwamnatin jihar dake birnin Benin, zai kasance karkashin jagorancin Dr. Ernest Afolabi Umakhine.

A yayin da Anslem Ojezua zai kasance mataimakin shugaban kwamitin, Frank Edebor zai zamo sakatarensa.

Sauran mambobin kwamitin sun hada Kassim Afegbua da Patrick Ikhariale da Taiwo Akerele da Patrick Idiake da kuma Rasaq Bello-Osagie. Har ila yau akwai karin mambobi irinsu Fredrick Unopah da Abdallah Eugenia da Patrick Obahiagbon da Kenny Okojie da Lindsey Tes-Sorea da kuma Abass Braimoh.

A jawabin daya gabatar yayin karbar rantsuwar kama aiki a ranar 12 ga watan nuwamban da muke ciki Okpebholo ya sha alwashin cewar gwamnatinsa za ta binciki yadda aka mayar da wasu ‘yan majalisar dokokin jihar 14 saniyar ware a 2019.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG