Halalliyar Majalisar Dokokin Libya Ta Yi Watsi da Daftarin Kafa Gwamnatin Hadin Gwuiwa

Libya

Majalisar dokokin gwamnatin Libya wacce hukumomin kasa da kasa suka amince da ita, tayi watsi da daftarin yarjejeniyar kafa gwamnatin hada kan kasa tareda daya bangaren masu ra'ayin addini.

Babu hakikanin dalilin da yasa suka yanke wannan shawara, sai dai wani rahoto yace 'yan majalisar sun fusata ne saboda masu ra'ayin addinin sunyi kwaskwarima ga yarjejeniyar ba tareda amincewar daya bangaren ba.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci duka sassan su sanya hanu kan yarjejeniyarkuma yayi barazanar aza takunkumi kan duk wanda ya nemi hana ruwa gudu.

A cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar jiya Litinin yace, "Akwai dukkan alamun cewa yarjejeneiyar zata warware matsalolin da Libya take fuskanta ta fuskar siyasa, tsaro, da wasu damuwa iri daban daban".

Libya tana fama da yamutsi da rikicin siyasa tun bayan da aka hambare gwamnatin mutumin da ya dade yana mulkin kasar Moammar Gadhafi aka kuma kashe shi a shekara ta 2011, wanda ya haifar da tarzoma, da ta'addanci, da rugujewar masana'antar man kasar.

Kasar ta dare gida biyu karkashin masu ra'yain Islama, wadanda suka kwace birnin Tripoli a bara suka kafa tasu gwamnatin, sannan ita dayar wacce duniya ta san da zamanta ta gudu daga birnin zuwa birnin Tobruk dake gabashin kasar.

Karkashin shirin na Majalisar Dinkin Duniya wakili Fayez Sarraj, daga majalisar dokokin da take Tripoli shine zai zama Firayim Minista. Sannan a nada masa mataimaka uku daga yammaci, da gabashin kasar, da kuma kudancinta.