Kotu a kasar Libya ta yanke hukuncin kisa ga Saif Al-Islam dan tsohon shugaban kasar Libya Moammaor Ghadaffi na rawar da ya taka lokacin da aka yi kiki kakan sauke mahaifin nasa daga kan karagar mulki.
Sai dai an yanke masa wannan hukuncin ne shi da wasu mutane 8 da suka hada da mai leken asiri zamanin gwamnatin Moamar Ghaddafi,wato Chief Abdallah Al-senousi da tsohon Firayim Ministan kasar Baghadadi al-Mahmoud..
Wani abun mamaki shi ne ba'a akawo Saif Al-Islam kotu ba domin yaji wannan hukuncin. Lokacin yanke wannan hukuncin yana hannun yan tawayen dake garin Zintan dake goyon bayan gwamnatin da aka amince da ita a duniya, amma ba wadanda keda goyon bayan masu tsattsauran raayin addini ba wadanda suke gudanar da harkokin gwamnatinsu a wajen babban birnin kasar na Tripoli.
Haka kuma kotun kasa da kasa tana nemanshi Saif din akan wasu tuhuma guda biyu da kotun take masa. Kotun ta kasa da kasa tace Saif din na daya daga cikin manya-manyan mutanen da suke da tasiri a lokacin gwamnatin mahaifin nasa
Kotun ta kuma zargi Saif da yin kokarin hana gudanar da zanga-zangar lumanar nuna kyamar gwamnatin mahaifin nasa wanda yayi anfani da hukuncin kisa kan masu zanga-zangar.