Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawaye Sun Afkawa Ofishin Jakadancin Nijer A Kasar Libiya


'Yan yakin sa kai a kasar Libiya
'Yan yakin sa kai a kasar Libiya

Wasu mayaka dauke da makamai sun kama ofishin jakadancin Nijer a Libiya daga la'asar zuwa karfe biyun dare

Wata bataliyar mayakan sa kai a kasar libya ta mamaye ofishin jakadancin kasar Nijer a birnin Tripoli ta tayar da hankalin ma’aikatan ofishin. Ko da yake babu asarar rayuka, amma mayakan sa kan sun jefa ma’aikatan ofishin jakadancin na kasar Nijer cikin rudu da fargaba wanda hakan ya sa ma’aikatar harakokin wajen kasar jamahuriyar Nijer ta kira wani taron manema labarai a birnin Niamey takamaimai don bayyanawa ‘yan kasa abun da ya faru.

Sakataren Ma’aikatar harakokin wajen kasar Jamahuriyar Nijer Mallam Abbani Ibrahim Sani ya shaidawa ‘yan jarida abun da ya faru a ofishin jakadancin na kasar Nijer a kasar ta Libiya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00
Shiga Kai Tsaye

Rahotanni sun ce mayakan sa kan na kasar Libiya sun yi hakan ne kawai domin su mayar da martani game da tsaurara matakan tsaron da gwamnatin kasar Nijer ta dauka a ofishin jakadancin kasar Libiya da ke Niamey, babban birnin kasar jamahuriyar Nijer.

Wakilin Sashen Hausa a Niamey Abdoulaye Mamane Amadou ne ya aiko da rahoton.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG