An soma wani sabon shirin tattaunawa tsakanin ‘yan gwagwarmaya da gwamnatin kasar Libya duk da cewa wasu sun yi garkuwa da mataimakin ministan harkokin wajen kasar.
A wani yunkurin lalubo zaren warware rikicin Libyan, Majalisar Dinkin Duniya tace za’a yi zaman tattaunawar sau biyu. Zaman farko za’a yishi a kasar Switzerland.
Dama can tawagar gwanmnatin Libya da Firayim Ministan kasar Abdullah al-Thani ya jagoranta ta zanta da ‘yan gwagwarmayar makonni biyu da suka gabata. To saidai kungiyar hamayyama fi girma bata kasance a taron ba.
Kungiyar ce ta cafke Birnin Tripoli bara lamarin da ya tilastawa Firayim Ministan al-Thani ficewa daga Birnin ya je ya kafa gwamnatinsa a gabashin kasar.
Ana cikin wannan sabon kokarin sasantawa sai kuma jiya Lahadi ‘yan bindiga suka cafke mataimakin ministan harkokin wajen kasar Hassan al-Saghir daga dakinsa a wani otel dake Birnin al-Baida. Jami’an gwamnati sun shaidawa manema labarai cewa ‘yanbindigan sun gayawa ma’aikatan otel din cewa su dakarun gwamnati ne.
Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin yin garkuwa da ministan.