Akalla mutane 8 suka rigamu gidan Gaskiya jiya Talata a Birnin Tripoli dake Libya biyo bayan wani harin da aka kai kan wani otel da ‘yan siyasa da ‘yan kasashen waje suka fi zuwa.
Jami’an kasar ta Libya sun bayyana cewa mutane biyar cikin wadanda suka mutu ‘yan kasashen waje ne sauran ukun kuma masu gadi ne.
Dangane da harin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka tace Ba’amarike daya na cikin wadanda aka kashe.
Kamar yadda jami’an gwamnarin Libya suka shaida, yan bindigan sun dana bam a wata mota da suka ajiye a gaban otel din da ake kira Corinthia kafin su afkawa ginin da harbe-harbe. Bayan sun gama sai ‘yan bindigan suka tarwatsar da kansu.
Wata kungiya mai suna Kungiyar Islama ta Yankin Tripoli ta dauki alhakin kai harin a cikin sanarwar da tayi ta yanar gizo. Tace harin ramuwar gayya ce cafke domin cafke Abu Anas al-Libi da dakarun Amurka suka yi a shekarar 2013.
Amurka ta kyautata zaton Al-Libi yana da hannu akan hare-haren da kungiyar al-Qaida ta kai kan ofisoshin jakadancinta dake Kenya da Tanzania a shekarar 1998.