Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LIBYA: An Bukaci Bangarorin Dake Gwagwarmaya Su Daidaita da Juna


Wakilan kungiyoyin Libya da na Majalisar Dinkin Duniya da manyan kasashe masu fada a ji wurin taron kawo zaman lafiya a kasar Libya
Wakilan kungiyoyin Libya da na Majalisar Dinkin Duniya da manyan kasashe masu fada a ji wurin taron kawo zaman lafiya a kasar Libya

Majalisar Dinkin Duniya da manyan kasashe maeu ikon fada a ji sun bukaci bangaorin dake hamayya da juna a Libya su daidaita domin a kafa gwamnatin hadin kai

Majalisar Dinkin Duniya da manyan kasashe masu ikon fada a ji, suna kira ga bangarorin hamayya a Libya su amince da yarjejeniyar raba daunin iko,su kawo karshen fada, da ta’addanci, da kuma fadi tashin siyasa da aka shafe kusan shekaru hudu ana fama da shi.

Jami’an diplomasiyan Majlisar Dinkin Duniya, da wadansu manyan jami’ai da suka gana jiya Laraba a Berlin sun fitar da sanarwar hadin guiwa cewa, yarjejeniyar warware takaddamar siyasar da za’a dama da kowa, ita ce kadai hanyar warware matsalolin Libya. Sun yi kira ga duk al’ummar Libya su kawar da shingayen da suka zama kadangaren bakin tulu domin a cimma yarjejeniya.

Sama da wakilan Libya ishirin suka je Berlin domin tattaunawar, da suka hada da jami’an diplomasiya daga kasashe masu kujerar din-din- din a kwamitin sulhu, da Kungiyar Tarayyar Turai, da Italiya, da Spain da kuma kasashen Afrika ta yamma da dama dake makwabtaka da Libya.

Libya ta shiga cikin rudani tunda aka hambare gwamnatin dadadden shugaban kasar mai mulkin kama karya Moammar Gadhafi, aka kashe shi a shekara ta dubu biyu da goma sha daya. Masu tsattsauran ra’ayin addinin Islama sun kwace Tripoli babban birnin kasar bara suka kafa kishiyar gwamnati da ta tilasa halar taciyar gwamnatin kasar gudu zuwa gabashin kasar.

Mayakan ISIS sun yi amfani da wannan tashin hankalin suka kwace yankin. Dubban ‘yan gudun hijira daga Libya dake kokarin gujewa tashin hankalin suna neman masu saffarar bil’adama su bi ta takun Bahar Rum dake tattare da hadari.

Yunkurin Manzon Majalisar Dinkin Duniya na musamman Bernardino Leon ya cimma tura, na neman hanyar cimma yarjejeniya cikin ruwan sanyi da bangarorin da suka yi fatali da shawarwarinsa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG