To amma wani wani jakadan Majalisar Dinkin Duniya Bernadino Leon yace bangarorin sun dukufa wajen cimma jituwa kan batun kafa gwamnatin hadin kan kasa cikin makwanni uku.
Mista Bernardino yace bangarorin biyu, wadda kowanne ke ikirarin iko da wani sashin kasar ta Libya da ya ki ya daidaita, ta lura cewa da bukatar a gaggauta yin wani abu game da tsaro a tattauwar da ake yi, sabanin halin da ake ciki a siyasance."
Libya dai ta dare tsakanin gwamnatoci biyu da ke samun goyon bayan mayakan da ke fada da juna. Gwamnatin da ke samun goyon bayan kasa da kasa ta na zama ne a birnin Tobruk da ke gabashin kasar, a yayin da kuma gwamnati mai kaifin kishin Islama ke mulki daga Trabulus babban birnin kasar.
Firaministan gwamnatin da ke Tobruk ya fadi ranar Talata cewa, zai sauka muddin jama'a su ka bukaci hakan. Abdullah Al-Thinni din ya fuskanci suka mai tsanani a wata hirar da aka yada ta gidan talabijin.
Inda jama'a masu tambaya su ka yi ta zargin gwamnati da kasa yin katabus. Sai yace yana iya murabus ranar Lahadi idan wannan ce mafitar da jama'a ke so.