Gwamnatin Nijar Ta Musanta Labarin Da Ke Cewa Bazoum Ba Ya Kwana A Fadarsa Bayan Juyin Mulkin Burkina Faso

Shugaba Bazoum Mohamed

Fadar shugaban kasar Nijar ta maida martani akan wata jita jitar dake cewa shugaba Mohamed Bazoum ya daina kwana a fadarsa tun ranar da sojoji suka yi juyin mulki a Burkina Faso.

A cewar masu yada wannan labari, shugaban na da fargaba game da yadda kwace mulki da karfin bindiga ke kokarin zama annoba a ‘yan watanni a kasashen yammacin Afrika.

Wani mai gabatar da labarai a tashar RTBF ta kasar Canada ya gwada taswirar guguwar juyin mulkin da ta taso a yammacin Afrika a ‘yan watannin nan bayan Mali, Guinea Conakry da Burkina Faso.

Ya ce an shiga halin fargaba a kasashe makwafta irinsu Jamhuriyar Nijar, har ma ya kara da cewa shugaba Mohamed Bazoum ya daina kwana a fadarsa tun a ranar da soja suka kifarda Roch Marc Christian Kabore.

Ganin yadda labarin ya fito daga wata kafar kasa da kasa ya sa wasu daga cikin ‘yan Nijar baiwa abin muhimmanci yayin da masu amfani da kafafen sada zumunta ke tafka mahawwara akai tsakanin wadanda ke kallon labarin a matsayin sahihi da wadanda ke daukarsa a matsayin shaci fadi.

Tuni dai fadar shugaban kasa ta karyatar da wannan labari ta hanyar wata sanarwar da ta fitar.

Kakakin jam’iyar PNDS Tarayya mai mulki Alhaji Assoumana Mahamadou na mai danganta wannan labari da abin da ya kira sabon salon da ‘yan siyasa suka bullo da shi da nufin cimma burinsu.

Amma Alhaji Doudou Rahama jigo a jam’iyar RDR Canji ta ‘yan adawa na cewa ruwa ba ya tsami banza, saboda haka wannan labari da ake yi wa kallon jita-jita wata manuniya ce ga shugabanin kasashe akan bukatar kwatanta adalci a tsakanin ‘yan kasa.

Kwana daya bayan ba da labarin abin da ya kira halin zullumin da shugaba Mohamed Bazoum ya shiga gidan television na RTBF ya sanar da cewa bayan da suka jiyo daga fadarsa shugaban kasar ta Nijar na nan daram bai kaura ba saboda haka kuskure aka yi wajen ba da wannan labari a cewar tashar mai ofishi a kasar Canada.