Hakan ya biyo bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban Alpha Conde da wani bangare na sojojin karkashin jagorancin Kanar Mahamady Doumbouya su ka yi.
Yankin a baya ya shirya yin taro kan wata majalisa ta musamman kan sake fasalin hukumomi, amma ya canza ajandar bayan juyin mulkin da aka yi a Guinea.
Duka ECOWAS da Tarayyar Afirka (AU) sun yi Allah wadai da juyin mulkin.
Paul Ijeme masanin harkokin kasa da kasa ne kuma tsohon jami'in ECOWAS. Ya gaya wa wakilin Muryar Amurka Peter Clottey cewa dole ne AU da ECOWAS su kasance da niyyar siyasa don tabbatar da cewa gwamnatocin Afirka suna da hakki kuma su cimma burin mutanen su.
Wannan, a zaman wani ɓangare ne na ƙoƙarin hana hambararwa daga hanun sojoji nan gaba da zaɓen gwamnatocin farar hula da tsarin mulki ya zaɓa.