Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Na Taron Gaggawa Kan Juyin Mulkin Sudan


Zauren Majalisar Dinkin Duniya
Zauren Majalisar Dinkin Duniya

Janar Burhan ya ce za su mika mulki ga gwamnatin farar hula a watan Yulin 2023, lokacin da za a gudanar da zabe na gama-gari.

Majalisar Dinkin Duniya na gudanar da taron gaggawa a ranar Talata don tattauna makomar kasar Sudan bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin wucin gadi.

Rahotanni sun ce jama’a da dama a Khartoum, babban birnin Sudan sun bazama kan tituna don nuna adawarsu da juyin mulkin.

Sojojin sun tsare Firai Minista Abdallah Hamdok da wasu jami’an gwamnatin majalisar da ke mulkin kasar.

A ranar Litinin Janar Abdel- Fattah Burhan ya ayyana dokar ta-baci sa’o’i bayan da suka rusa majalisar mulkin kasar wacce ke kunshe da sojoji da fararen hula.

Tun a watan Agustan 2019 aka kafa gwamnatin bayan da hambarar da dadadden tsohon shugaban kasar Omar Al-Bashir.

Yayin jawabin da ya yi ta kafar talabijin, Janar Burhan ya ce ya rusa gwamnatin ne saboda “rikicin siyasa da ya kunno kai, yana barazana ga tsaron kasar, inda ya ayyana cewa, “nan ba da jimawa ba za a kafa sabuwar gwamnatin mai dauke da kwararru.”

Ya kuma yi alkawarin cewa sojojin za su mika mulki ga gwamnatin farara hula a watan Yulin 2023, lokacin da za a gudanar da zabe na gama-gari.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG