Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Ke Janyo Juyin Mulki a Kasashen Afirka: Mahaman Ousman


Mahamman Ousman
Mahamman Ousman

Tsohon shugaban kasar Nijar Mahaman Ousman wanda hukumar zabe ta bayyana a matsayin wanda ya sha kasa a zagaye na 2 na zaben da ya jaddada aniyar bin hanyyoyin lumana wajen gwagwarmayar kwato abinda ya kira galabar da ya samu a wannan zabe.

A hirarshi da Aliyu Mustapha Sokoto dan takarar na RDR Canji ya ce za su bi hanyoyin da doka ta ayyana na yin abinda ya kamata, a maimakon tayar da hatsaniya sabanin ra’ayin da wasu magoya bayansa ke nunawa akan wannan dambarwar.

Tsohon shugaban kasar ya musanta jita jitar barakar da ake cewa ta kunno kai a tsakanin shugabannin jam’iyyun kawancen adawa. Ya ce a bakin 'yan jarida ya ke jin cewa akwai baraka, amma bisa ga saninsa, babu wani abu makamancin haka. Ya bayyana cewa, kafin zaman tattaunawa da Sashen Hausa sun yi taron jam'iyyar da ya sami halartar mutane da dama.

Hotunan zanga zangar da aka gudanar a birnin Yamai na Nijar, bayan hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa.
Hotunan zanga zangar da aka gudanar a birnin Yamai na Nijar, bayan hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa.

Dangane da batun cewa, wadansu 'yan jam'iyyar hamayya sun so a dauki wani mataki dabam na nuna kin amincewa da sakamakon zaben, tsohon shugaban kasar ya ce a matsayinshi na dan takara, yana da wadansu damarmaki da zai iya daukar matakin kalubalantar zaben ta hanyar lumana ba ta tashin hankali kamar yadda wadansu su ka fara ba.

Bisa ga cewarshi, matakan da zai iya dauka a ganinshi, suna da kwari sun fi ya fito ya yi ta hayani da tashin hankali shi kadai ko kuma tare da wadansu ba. Ya ce shi kanshi zaben, yana da ka'idoji, dalilin kenan da za a iya tabbatar da sahihanci ko kuma rashin sahihancinsa. Sabili da haka idan aka ga an saba wa ka'idar zaben, sai a bi tsarin da doka ta tanadar na ganin an yi abinda ya dace.

Hotunan zanga zangar da aka gudanar a birnin Yamai na Nijar, bayan hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa.
Hotunan zanga zangar da aka gudanar a birnin Yamai na Nijar, bayan hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa.

Bisa ga cewar, tsohon shugaban kasar Mahaman Ousman, su kansu masu sa ido na kasashen waje sun ga kurakuran da aka tafka a zaben, suka kuma bada hakuri tare da kira ga 'yan jam'iyun hamayya su bi hanyoyin da doka ta tanada na kalubalantar zaben.

Ya bayyana cewa abin da ya janyo juyin mulki a kasashen Afrika kwananan nan, ba wani abu ya haifar da su ba illa take tsarin mulki da taka dokoki da kuma magudin zabe.

Ya ce shi mai son kare kasar shi ne da kuma damokaradiya. Yana kuma son ganin an yi komi cikin kiyaye hakkin kowane dan kasa.

yan-hamayya-sun-kalubalanci-gwamnatin-mohamed-bazoum

ko-bazoum-zai-iya-magance-rikicin-siyasar-nijar

ba-za-mu-lamunci-juyin-mulki-a-afirka-ba-ya-zama-tsohon-yayi---buhari

Saurari hirar cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG