A yayin da aka shiga halin rashin tabbas a kasar Burkina Faso inda rahotanni ke cewa sojoji sun kifar da shugaba Roch Mark Christhian Kabore bayan wata tarzomar soja akan bukatar samun kayan yaki domin tunkarar kungiyoyin ta’addanci, masu rajin kare dimokraiya a jamhuriyar Nijar sun bayyana takaicinsu a game da yadda dimokradiya ke fuskantar barazana a mafi yawancin kasashen Afrika.
Har I zuwa karfe 2 na ranar yau Litinin babu tabbaci game da abubuwan da suka faru da shugaban kasar Burkina Faso Roch Mark Christian Kabore inda rahotanni sanyin safiya ke cewa, sojoji na tsare da shugaban a wani barikin sojan birnin Ouagadougou.
Wasu majioyi a Burkina Faso sun yi nuni da cewa, akwai alamar rarrabuwar kawuna a tsakanin dakarun kasar mafari ake fuskantar jan kafa wajen sanar da jama’a abinda ke faruwa a zahiri tun bayan tarzomar ta sake barkewa a wasu barikokin soja a cikin daren jiya Lahadi zuwa wayewar yau Litinin.
Shugaban wata kungiyar kare dimokradiya a Nijar Inoussa Saouna na mai kalobalantar wannan al’amari da ke nuna alamun yunkurin shimfida mulkin kama karya a kasashen yammacin Afrika.
Kawo lokacin hada wannan rahoto, bayanai daga birnin Ougadougou na cewa sojoji sun girke tankokin yaki a mashigar gidan rediyo da talabijin mallakar gwamnatin Burkina Faso wato RTB yayin da suke ci gaba da watsa shirye shirye kamar yadda suka saba a wani lokacin da jama’a ta shiga cikin halin rudani.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: