A cikin hirarshi da shugaban Sashen Hausa Aliyu Mustapha, Bazoum ya bayyana cewa, duk da haka, a wadansu lokuta rashin sanin mahimmancin damokaradiya na sanya wasu zumudin karbar mulki da karfin soja kamar yadda aka yi yunkuri karshen watan Maris da ta gabata a Jamhuriyar Nijer kwanaki 2 kafin ya yi rantsuwar kama aiki.
Shugaba Bazoum ya ce har yanzu akwai wadanda basu yarda da damokaradiya ba a Jamhuriyar Nijar, dalili ke nan wadansu su ka yi yunkurin juyin mulki a kasar kwanaki biyu kafin rantsar da shi, ya kuma bayyana cewa, wadanda su ka yi yunkurin juyin mulkin sun yi kokari ne su hana shi hawa karagar mulki kasancewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Yusuf wanda ya gabace shi ya kammala wa'adin mulkinsa. Sai dai yace bayan watanni bakwai yana mulki yanzu 'yan asalin kasar sun fara gane ko wanene shi da kuma manufofinsa.
nijer-matsalar-tsaro-ke-ta-sha-kanmu--bazoum-mohamed
Dangane da juyin mulkin da ake yi a wadansu kasashen nahiyar Afrika, Shugaban kasar na Jamhuriyar Nijar ya ce idan aka lura da juyin mulkin da aka yi a kasar Guinea, za a lura da cewa, shugaban kasar da aka yi wa juyin mulki shi ma juyin mulki yayi. Bisa ga cewarshi al'ummar kasar ba su da wata mafita, face yin juyin mulki. Yace idan ma an dauka an zabe shi ne kasancewa ya tsaya takara karkashin tsarin damokaradiya, sai dai bayan cikar wa'adin mulkinsa ya yi amfani da karfin iko ya ci gaba da mulki ya kuma yi amfani da makaman da ya mallaka ya rika kashe kashen mutane, sabili da haka bai zama da mamaki ba da aka yi mashi juyin mulki."
Shugaba Bazoum Mohammed ya ce "duk wanda ya yi amfani da karfi ya zauna, bai da kowacce shari'a. In aka yi mashi juyin mulki, dabam ne da gwamnatin wanda zababbiya ce."
Dangane kuma da juyin mulkin kasar Mali, shugaban na Jamhuriyar Nijar ya ce, matsalar ta'addanci da gudanar da mulki, wanda bai dace ba, su suka yi sanadiyar juyin mulki. Yace sojoji sun kwace mulki a kasar sabili da aganinsu ya zama wajibi ne su karbi mulki. Sai dai ya kamata su tsayar da lokacin da za a gudanar da zabe, domin a sami mutanen da al'umma ta zaba su ci gaba da mulki bisa ga tsarin damokaradiya. Sai dai sabanin haka ake gani, domin sun kwace mulki, kuma za su ci gaba da rike shi da karfi.
Shugaba Bazoum Mohammed ya ce "abinda ya haifar da juyin mulkin Sudan shi ne yadda wadanda da farko aka yi wa juyin mulkin ba su sauka ba, wadanda suka zo basu rike gaba daya ba suka raba shi gida biyu suna zaman gambiza" bisa ga cewar shi, wannan yanayin ya iya bada iza wadanda su ke ganin basu da tasiri su kwace mulki.
Saurari bayanin nasa cikin sauti:
voa-za-ta-hada-kai-da-kafafen-yada-labarai-a-najeriya
muryar-amurka-ta-kulla-yarjejeniya-da-kafofin-yada-labarai-a-jihar-adamawa
voa-za-ta-bude-ofis-a-arewa-maso-gabashin-najeriya