Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam Gwarzo wanda ya yi zargin ya nemi afuwar Malam Nuhu Ribadu.
Aminu Abdulsalam ya bayyana cewa yaudarar gwamnatin aka yi kan bayanan da aka ba ta wanda hakan ya sanya ta zargi Ribadu da hannu wajen dawo da Aminu Ado Bayero zuwa Kano.
Dama dai a karshen mako ne mataimakin gwamnan jihar Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zargi Ribadu da hannu wajen sake komawar tubabben sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero jihar.
Tuni dai Nuhu Ribadu ya karyata wannan zargin, tare da barazanar daukar matakin shari’a akan mataimakin gwamnan.
A lokacin da mataimakin gwamnan na Kano Aminu Gwarzo ke ganawa da manema labarai a fadar gwamnati a jiya Lahadi ya nemi afuwar Ribadu, inda ya ce an samu matsala ne daga bayanan da aka basu.
"Ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara ya musanta zarge-zargen da muka yi. Na gani a gidajen jarida uku kuma na ga maganar cewa za su kai kara kotu," a cewar mataimakin gwamnan.
"Mun zurfafa bincike kuma mun gano cewa an yaudare mu ne da bayanan, don haka a madadin gwamnatin jihar Kano muna neman afuwar NSA."
Mataimakin gwamnan ya kuma baiwa Ribadu tabbacin ci gaba da bashi hadin kai, wajen gudanar da aikinsa a matsayinsa na mai baiwa shugaban kasa shawara.